Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Horaswar Bautar Kasa Lokacin Dogaro da Kaine


matasa masu yima kasa hidima
matasa masu yima kasa hidima

A lokuttata da dama mutane basa amfani da damar da suke da ita don tallafawa kansu dama al’umarsu baki daya. Tsari da ake da shi a Najeriya na matasa suyima kasa hidima bayana kamala karatun su na jami’a, wani abu ne me matukar mahimanci, musamman ma idan wadannan matasan sunyi amfani da wanna horaswar ta yadda ya dace.

Wato shi dai wannan tsari na yima kasa hidima da akansa matasa maza ko mata suyi yana da matukar amfani, tayyada yake bama wadannan matasan damar sanin makamar aiki da ma sanin abun da duniya keci, ta inda zasu je wasu garuruwa da basu taba zuwa ba, don yin aiki ga gasa.

A irin haka ne sai ga wani matashi me suna Abdulrahman Balarabe Isah, wanda yake amfani da wata dama don tallafama kanshi batare da ya dogara da gwamnatiba, shi dai wannan matashin a lokacin da yake gudanar da aikin bautar kasanshi ya kasance yana hadawa da sana’a ne wanda yakan siya kayyayaki da suka hada da kayan sawa da turaruka yana kaiwa inda yasan matasa ‘yanuwanshi suke don sai damusu.

Kuma wannan matashin ya bayyanar da cewar yakan samu alheri matuka a wannan kasuwanci, kuma yana kara kira ga matasa da su meda hankali wajen samun abunda zasu dinga dogaro da kansu batare da sun jingina ga gwamnatiba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG