Lamarin 'Yan Boko Haram Ya Tayarwa Da Wasu 'Yan NIjar Hankali

Wasu mazauna kauyukan dake kan iyakar kasar Nijar da Burkina Faso, sun fara tserewa daga matsugunansu, sakamakon yanayin dar dar din da aka shiga a wannan yanki dake matsayin wata malaba ga ‘yan ta’addan kasar Mali.

Rahotanni daga kauyen Boni na gundumar Torodi sun bayyana cewa daruruwan mutane ne suka tserewa tashin hankalin, da ake fuskanta a garuruwan dake kan iyakar Nijar da Burkina Faso.

Yankin da ake dauka a matsayin wata maboyar ‘yan ta’addan Arewacin Mali kamar yadda wakilin kungiyar Transparency a garin Makalondi Malan Habibou ya shaida ma Muryar Amurka ta wayar tarho.

Da jin wannan labarin hukumomin Nijar suka kira wani taron gaggawa a birnin Yamai, wanda ya hada wasu gwamnoni da wakilan kungiyoyin agaji na kasa da kasa, domin kai dauki ga wadanan ‘yan gudun hijirar, a cewar ministan ayyukan jin kai Alhaji Lawan Magaji a zantawarsa da muryar Amurka.

Yankin Tilabery mai makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso na daga cikin yankunan dake karkashin dokar ta baci a Nijar, sakamakon yawaitar ayyukan ta’addanci, yayin da wasu kasashe 5 na yankin Sahel suka kafa rundunar hadin gwiwar G5 Sahel da nufin kakkabe masu tayar da kayar baya,

Sai dai tsaikon da ake fuskanta wajen shigowar kudaden da kasashen duniya suka yi alkawalin bayarwa na tauye harkokin gudanarda wannan runduna.

Wakilin muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko muna da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jama'a Da Dama Na Gudun Ceton Rai A Jamhuriyar Nijar 3'20"