Lamari Na Kara Tabarbarewa a Syria

Wata mata tare da yara na gudun neman tsira biyo bayan harin dakarun gwamnatin Syria a yankin Ghouta.

Kungiyar dake bin diddigin yakin Syria tace yau Talata dakarun dake goyon bayan gwamnati dake rike da birnin Damscus sun kaiwa gundumar Ghouta hari, sun kashe akalla mutane 45, a ci gaba da tashin hankalin da ya biyo bayan wani farmakin da aka ce shine mafi muni da aka kai a yankin tun shekarar 2015.

Kungiyar kare hakkin bil Adama dake sa ido a Syria da ake kira “Observatory”, ta fada jiya Litinin cewa, hare-hare ta sama da ruwan bama-bamai sun kashe kusan mutaen 100.

Gabashin Ghouta dai shine yankin na karshe da ‘yan tawaye ke da karfi a cikinsa a kusa da babban birnin Syria, kuma fadawa cikin tashin hankalin ya janyo damuwa daga kasashen duniya.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta nuna damuwarta yau Talata, tana mai cewa ta kafar Twitter, “Wannan abu ba zai ci gaba ba”

Panos Moumtzis, Jami’in kula da aiyukkan badaagaji na Majalisar Dinkin Duniya a Syria, ya fadi a wata sanarwa jiya Litinin cewa, lamari ya sake tabarbarewa a Syria.