A yayin da zanga-zangar neman gwamnati ta kawo karshen tsadar rayuwa ta kara rikidewa zuwa wani abu na daban, musamman ma a jihohin arewa, har ya kai ga daukar matakin sanya dokar hana zirga-zirga a Kaduna, Kano da Filato, masu fada a ji a arewacin Najeriya sun yi kira ga matasa da su guji aikata barnar da za ta kara mayar da yankin baya, tare da cewa lalata kadarorin gwamnati da na al’umma ba zai haifar da da mai ido ba.
Zanga-zangar lumanar, wacce aka fara a ranar 1 ga watan Agustan nan da muke ciki dai, ta sauya salo ne daga yini na biyu a jihohin Kano, Kaduna, Borno, da Neja, inda wasu gungun matasa suka fara afka wa ma’aikatun gwamnati da shagunan ‘yan kasuwa da ba su ji ba ba su gani ba, lamarin da ya kara muni a yini na Biya har ya kai ga sanya dokar hana zirga-zirga a jihohin Kaduna da filato, wanda a yini na biyu aka saka irin wannan dokar a jihar Kano.
Ababen da su ka fi sanya fargaba a zukatan wasu ‘yan kasa da ma jami’an gwamnati su ne yadda masu zanga-zangar su ka farfasa shaguna, afka ma wasu jami’an tsaro, tare da kwace wata motar yaki, baya ga daga tutar kasar Rasha tare da ambaton neman shugaba Putin ya kawo musu dauki.
Tuni dai wasu ‘yan kasa su ka fara tofa albarkacin bakinsu a kan batun daga tutar kasar Rasha, inda mai sharhi a kan al’amurran ‘yau da kullum, Abubakar Muhammad Abujega, ya ce ba abun daga hankali a batun daga tutar Rasha illa kawai gwamnati ta saurari koken al’umma don samo mafita mai dorewa, inda ya kara da cewa, idan alkhairi ne sojoji su karbi mulki, sai ‘yan kasa su ci gaba da addu’a.
Saidai, shugaban kungiyar one Nigeria, mai rajin tabbatar da cewa ‘yan kasa sun hada kai wajen neman ci gaba su zama tsintsiya daya madaurinki daya, Alh. Muhammad Saleh Hassan, ya bayyana cewa barnata dukiyar al’umma da sunan zanga-zangar ba zai Haifar da da mai ido ba, ya na mai yin kira ga matasan da su san cewa su ne yau da kuma goben Najeriyar.
Shi ma tsohon kwamishinan yada labarai da tsare-tsare a jihar Adamawa, Alhaji Ahmad Sajoh ya ce abunda da ke faruwa a jihohin arewa abun bakin ciki ne, kuma babu riba a yin barna ga dukiyar gwamnati, yana mai cewa dole ne al’ummar arewa su farga kuma gwamnati ta dauki matakan da suka dace cikin gaggawa don dakile ci gaba da yin barnar da ake gani.
A kusan duk lokacin da aka sami matsalolin tattalin arziki da suka kai ga gudanar da zanga-zanga a arewa, ba’a wanyewa lafiya inda a shekarun baya ma an yi zanga-zangar da suka yi sanadin kashe-kashe, da lalata dukiyoyin al’umma, lamarin da masana suke cewa kamata ya yi masu ruwa da tsaki a arewacin Najeriya su sake nazari don neman mafita mai dorewa ga yaki da dabi’ar mayar zanga-zangar zuwa rikici da ke kawo koma baya ga yankin.
Daga Halima Abdulra'uf, Abuja, Najeriya.