Lahadin nan za'a yi zaben fidda gwani a kasar Senegal

Tsohon Prime Ministan Senegal Macky Sali, dan takara a zaben fidda gwani

Yau Lahadin nan idan Allah ya yarda za’a yi zaben fidda gwani a kasar Senega, tsakani shugaba Wade da tsohon Prime Minista Macky Sali.

Yau Lahadin nan idan Allah ya yarda za’a yi zaben fidda gwani a kasar Senegal. Jiya asabar jajibirin zaben, jami’an kasar suka bukaci a kwantar da hankali a zaben fidda gwanin da masu hamaiya wadanda suka hada kai zasu yi kokarin hanna shugaba Abdoulaye Wade dan shekara tamanin da biyar da haihuwa samun nasara a wa’adin mulkinsa na uku.

Abokin hamaiyarsa Macky Sali tsohon Prime Minista yayi hasashen cewa shine zai lashe zaben. Shi dai Mr Sally ya dogara ne akan cikakken goyon bayan da masu hamaiya suka bashi. Shima shugaba Wade yayi has ashen shine zai lashe zaben.

In dai ba’a mance ba, shawarar da shugaba Wade ya yanke na sake tsayawa takara a karo na uku ta haddasa zanga zangar sosai a kasar ta Senegal a farkon wannan shekara. To amma ganin cewa har za’a yi zaben fidda gwani tasa masu hamaiya ke fatar kada shi.