Sabon shugaban kasar Senegal, Macky Sally a yi rantsuwar kama mulki, al’amarin da ya kai dadadden shugaban kasar Abdoulaye Wade ga mika mulki ba wata-wata.
An rantsar da Mr. Sall a gaban dubban manyan mutane a cikin wata rumfar da aka kawata da launin tutar kasar Senegal mai ja da tsanwa da kore.
A zagayen fidda gwanin da aka yi ranar 25 ga watan Maris, Mr. Sall ya yi galaba a kan tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade, da kimanin kashi 65 cikin dari na kuri’un da aka kada.
Mr.Wade ya hasala ‘yan kasar Senegal masu dimbin yawa lokacin da ya yanke shawarar neman wa’adin mulki na uku, duk kuwa da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya takaita shugabancin kasar ga wa’adi biyu kawai. Tarzomar da hakan ya janyo ta yi sanadiyar mutuwar mutane 6 a kasar Senegal.
Rungumar kaddarar da Mr.Wade ya yi bayan kayen da ya sha a zaben fidda gwani ya kara jadadda ficen da kasar Senegal ta yi a matsayin kasa mai tsayayyar demokradiya.
Shugaba Macky Sall ya na da shekaru 51, kuma a can baya ya yi shekaru uku ya na rike da mukamin firai minista a karkashin mulkin tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade.