Augustine Bangong wanda aka fi sani da 'Bom’ mawakin hip-hop wanda ya ce abinda ya ja hankalinsa ga waka shine, ya taso cikin yanayi na rikice-rikice kasancewar a garin Jos ya tashi.
Bom ya ce waka wata hanya ce ta isar da sako ga al'umma, mussaman ma a lokutan da ake bukatar hakan, ya ce yana isar da sakonnin zaman lafiya da kwanciya hankali, da kuma illolin da ke tattare da rashin kwanciyar hankali tsakanin al'umma.
Ya kara da cewa tun lokacin da ya tashi, babban burinsa dai shine ya fadakar tare da nishadantar da al'umma, Najeriya kasa ce mai cike da kabilu daban daban da banbance banbance addinai wanda zaman lafiya ne kadai zai kawo cigaban kasar.
Akasarin wakokinsa duk da dai cewar basu da yawa amma a nan kusa zai fitar da su, ya kara da cewa samun tallafi da taimako a cikin alumma yanzu yana da matsaloli da dama kasancewar akwai karanci taimako.
Masana’antar waka ta na taimakawa amma ba yadda mawaka masu tasowa ke bukata ba, ya ce babban burinsa shine ya fitar da kalmomin da ke ran sa don duniya tayi sanyi, ta hanyar isar da sakonnin da suka kamata.
Your browser doesn’t support HTML5