LAFIYARMU: Hadarin Dake Tattare Da Gurbattacciyar Iska Da Mutane Ke Shaka A Yau Da Kullum

Your browser doesn’t support HTML5

Bisa kididdigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, kusan dukkan mutane a duniya suna shakar iskar da ta zarce ka'idojin ingancin iska na hukumar lafiya ta duniya – wato isa da take a gurbace. Wannan gurbacewar yanayi na da illa ga lafiyar dan adam.