Tashe tashen hankula da kisan gilla da ake yiwa ‘yan Najeriya na ci gaba da samar da yara marayu wadanda idan ba'a kula da su ba suna iya fuskantar mummunan rayuwa wadda sukan iya fadawa ga ayukkan da suma za'a koka dasu nan gaba.
To sai dai wasu daga cikin wadannan yaran sun samu gata suna samun cikakkar kulawa kuma ba da jimawa ba wasu marayun zasu samu irin wannan gata.
Tun lokacin da aka soma samun tashe tashen hankula da kashe kashen mutane barkatai a Najeriya ake samun yara marayu wadanda suka rasa gata.
Matsalar wadda ta fara a arewa Maso gabashin Najeriya yanzu ta game dukan arewacin kasar har ma da wasu sassan kudanci.
Wadannan yaran a cewar masanin halayyar Dan Adam Farfesa Tukur Muhammad Baba rashin kula dasu ba yana illa a cikin al'umma .
Yanzu kimanin shekara uku da wani mai ayyukan jinkai a Sakkwato Umarun kwabo AA ya buda makaranta mai suna JARMA UK ACADEMY wadda aka samar domin kulawa da marayu wadda yanzu haka ke dauke da yara sama da 160 da aka dauko daga jihohin Borno, Yobe da wasu daga Sakkwato kuma yaran sun ce rayukansu sun inganta.
Kulawa da maraye dai abu ne mai muhimmanci wanda shugabanni ke ta jawo hankulan jama'a akai wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya nuna bukatar a kula da yi.
Gwamnatin jihar Sakkwato tana bayar da gudunmuwa ga wannan makarantar abinda yasa Wanda ya assasa ta ya kudurci kara dauko wasu marayu .
Hukumar zakkah da wakafina cikin hukumomi masu hidima ga marayu a Najeriya, acewar shugaban ta Muhammad Lawal Maidoki wannan wani nauyi ne aka dauke musu.
Idan aka ci gaba da samun masu kulawa da marayu kamar wannan abin kan iya kawar da duk wata matsala da ake ganin rashin kula dasu kan iya haifarwa.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5