Kyanwa Ta Farko A Duniya Da Taci Gajiyar Kafar Zamani Ta 3D

Wasu dalibai a jami’ar Wisconsin-Madison sun kirkiri kafar zamani ga wata Mage.

A ‘yan watannin bayane wata kyanwa ta hadu da hadarin jirgin kasa, hadarin da yayi sanadiyyar rasa kafarta ta baya. Wata kungiya mai rajin kare hakkin dabbobi mai suna Adam Schofield ta dauki magen don bata kulawa da ta dace.

Daga bisani taron wasu dalibai a jami’ar Wisconsin-Madison dake nan kasar Amurka sun yima wannan kyanwar kafar zamani.

Daliban sun yi amfani da naurar zamani da ake kira 3D printer, wajen kirkirar wannan kafar, da zata taimakawa magen wajen tafiya ba tare da tana dingishi ba.

Kyanwar na tafiya daban da yadda sauran maguna ke tafiya a sanadin hadarin, amma wannan sabuwar kafar da akayi ma magen, na taimakawa magen wajen tafiya kamar sauran maguna.

Fasahar 3D printer, na daukar hoton abu da fitar da shi kamar yadda na asalin yake, tana kuma amfani da karfe, roba, auduga wajen fitar da abubuwan da ake bukata, batare da samun wata matsalaba, wannan itace sabwar hanyar cigaban kimiyya da fasahar zamani a karni na 21.