WASHINGTON D.C. —
Cibiyar binciken magunguna daga tsirrai ta Afirka da ke jami’ar Jos, ta kirkiro rigakafin da zai kare mutane da dabbobi daga dafin sarar maciji.
A cewar masanan, rigakafin zai kuma kare mutane daga dafin kunama, gizo-gizo, kudan zuma da makamantansu.
Jagorar masu binciken, Farfesa John Aguiyi, ya ce ya fara gudanar da binciken rigakafin ne saboda rage rasa rayuka da sarar macizai ke haddasawa.
A cewar, Farfesa Abraham Dogo, rigakafin zai magance dafin kowane irin nau’in maciji.
Shi ma Farfesa Abwoi Madaki, ya ce rigakafin mai suna COVI-PLUS, allura ce da aka samar don kariya.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos:
Your browser doesn’t support HTML5