Matsalar shaye-shaye a tsakanin al’umma na daga cikin dalilan da ke haddasa karuwar masu tabin hankali a Najeriya, kamar yadda bincike ya nuna.
Ma'aikatar lafiya ta ce akalla akwai masu tabin hankali tsakanin miliyan 40 zuwa miliyan 60 cikin al’ummar kasar da yawansu ya kai miliyan 200, da ke kasar.
A cewar Evangelist Joel Hammajulde Gashaka, da ke aikin kula da masu tabin hankali da wasu cututtuka a garin Lafia, fadar Jihar Nasarawa, matakan da gwamnatin tarayya ta dauka na hana ta’ammali da maganin Tramadol, ya saukaka yawaitar wadanda ake kawo masa don taimaka ma su.
Idi Uba Suleiman wanda ya sami tabin hankali ta hanyar shaye-shayen miyagun kwayoyi ya ce ya fara shaye-shayen ne don ya sami marmarin cin abinci.
Ita ma Lydia Shikku ta ce a wani lokaci can baya har ta kashe jaririyarta saboda ba ta san halin da ta ke ciki ba.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos:
Your browser doesn’t support HTML5