Zuwa karshen watan Maris din bana, shafin hukumar kula da bashin Najeriya, a yanar gizo ya nuna ana bin gwamnatin tarayyar Najeriya da jihohi bashin ketare, da na cikin gida dala biliyan $81,274 wanda ke daidai da Naira tiriliyan ₦24.947.
Basussukan da suka kama daga na bankin raya kasashe na Afirka, da bankin duniya, da bankin Exim na Sin da Indiya, har ma da lamuni daga kasar Jamus.
Masanin tattalin arziki Elharoun Muhammad ya ce Najeriya ta fada wannan jibgin bashin ne don yadda ta ke aiki da hanyoyin hukumar lamuni ta duniya, wato IMF.
Shi ma masanin tattalin arziki Abubakar Ali, ya ce matukar a na ci gaba da dogaro da dala wajen sayo kaya a ketare, to ba za a fita daga hanyar bashi ba. Kuma sai an dawo da raya tattalin arziki, daga lamuran cikin gida.
Shi kuma masanin tattalin arziki Yushau Aliyu ya ce ba laifi in za a yi amfani da bashin ta hanyar samarwa al’umma sauki da rage matakan tattalin arziki masu amfana.
Kasafin kudin da a ke ciki, ya nuna Najeriya za ta hako man fetur ganga miliyan 2 da dubu 200, wanda idan hakan ya dore zai iya samawa kasar kudin da za ta iya amfani da su, don rage karbar karin bashi.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5