Yayin da sabbin manyan shugabannin rundunonin sojojin Najeriya da shugaba Buhari ya nada suka kama aiki, masu sharhi kan harkar tsaro na ganin, kamata ya yi, a yi dokar da za ta rika sakawa manyan hafsoshin wa’adi, don gujewa zamansu a mukamin na tsawon lokaci da bai kamata ba.
“Wasu kasashe ba ma za a tsaya ana rigima ba, saboda shi kansa shugaban kasra akwai dokar da aka saka ma shi cewa idan mutanan nan suka yi shekara kaza za a cire su, idan kuma za ka kara musu ne sai aka saka ka’idojin da dole sai sai suna ciki sannan za a kara musu,” wa’adi. In ji Group Captain Sadiq Garba mai ritaya.
A farkon makon nan ne dai shugaba Buhari ya sauke manyan hafsoshin sojin kasar, duk da cewa a baya, ya ki jin kiran da jama’a da ‘yan majalisar dokoki suka yi ta masa na ya sauke su.
Kimanin shekaru biyu kenan 'yan Najeriyar ciki har da 'yan majalisar dattawa da wakilai ke fatar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kwabe manyan hafsoshin daga mukamin su.
Duk da mutane na cewa an makara amma da babu gara ba dadi, sun yi fatar shugaba Buhari a sauran wa'adin sa na mulki zai rika daukar shawarar jama'a kan muhimman lamura.
Dan majalisar wakilai Kasimu Bello Maigari ya ce duk da azamar shugaba Buhari ta yin aiki amma karewar basirar tsoffin hafsoshin ya hana samun nasara kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Hakanan shi ma sakataren labarun APC a Jihar Kebbi Alhaji Sani Dododo ya kyautatawa shugaban tunani cewa ba mamaki ya na jiran sai lokacin da ya dace ne ya jawo jinkirin sauyin.
Ana kyautata fatar sabbin hafsoshin karkashin tsohon kwamandan rundunar yaki da boko haram Janar Leo Irabor za su dage wajen sauya lamuran tsaro da su ka tabarbare don kar jama'a su dawo daga rakiyar rundunar.
Ga Hauwa Umar da karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5