Korafin muzgunawa jama’a yayin gudanar da ayyukan su shine abin da masu zanga zangar suka zargi jami’an rundunar ‘yan sandan ta SARS, kuma neman rusa rundunar na daga cikin bukatun su.
Ko da yake hukumar ‘yan sandan kasar ta sanar da rusa rundunar tare da maye gurbinta da wata da aka lakabawa suna SWAT, amma masu zanga zangar sun ci gaba.
Dr Nasiru Adamu Aliyu wani lauya mai zaman kansa a Kano kuma Malami a Jami’ar Bayero Kano ya ce akwai bukatar samar da cibiya ko hukuma mai karfin gaske da za’a dorawa nauyin ladabtar da ‘yan sanda a najeriya kwatankwaci wacce ake da ita a Burtaniya.
Ya ce kamar yanda ake da sashin binciken jami’ai a ma’aikatu da dama kamar na kiwon loafiya da sauran su, ya kamata a kuma samar da wani sashe na musamman da zai bincike ‘yan sanda masu aikata laifuka kana ya gurfanar da su a gaban kotu domin jan kunnen su.
A nashi bayanin, Sanata Masa’udu Eljibiril Doguwa tsohon wakili a majalisar dattawan Najeriya ya ce tilas ne gwamnati ta dauki matakan hana matasa zanga zanga.
Ya ce rufe makarantu na cikin manyan dalilai da yasa matasa zanga zanga, domin haka dole ne gwamnati ta duba bukatun malamai domin su koma makaranta a ci gaba da karatu.
Batun samar da horo ga ‘yan sandan Najeriya na daga cikin al’amuran da masana ke ganin wajibi a baiwa kulawa yayin yiwa rundunar ‘yan sandan Najeriya garanbawul.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5