Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Zai Gana Kan Rikicin Lebanon

  • VOA Hausa

Israel Palestinians UN Security Council

Taron dimbin shugabannin kasashen duniya, wanda ya kasance kololuwar gangamin diflomasiya, na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Lebanon ke cewa hare-haren isra’ila sun hallaka mutane 558, 50 daga cikinsu yara kanana.

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa akan kazancewar rikici a Lebanon, a cewar jakadan Slovenia a majalisar, kasar dake rike da shugabancin karba-karba na kwamitin.

Tunda fari a jiya Talata, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya gargadi shugabannin duniya da cewar Lebanon na daf da afkawa cikin yakin yayin da hare-hare ke kara kazancewa tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullahi gabanin shugaban Amurka ya gabatar da jawabinsa na bankwana a babban taron majalisar dake gudana a duk shekara.

Taron dimbin shugabannin kasashen duniya, wanda ya kasance kololuwar gangamin diflomasiya, na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Lebanon ke cewa hare-haren isra’ila sun hallaka mutane 558, 50 daga cikinsu yara kanana.

Yayin da shugabannin duniya suka hallara a Manhattan domin gabatar da jawabai da ganawar diflomasiya ta gani ga ka, mamba a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya Faransa ta bukaci a gudanar da taron gaggawa a Litinin data gabata akan wutar rikicin dake kokarin mamaye yankin gabas ta Tsakiya.

A yayin da adadin mutanen da hallaka a Lebanon ke karuwa, hankula sun kauce daga kan abinda ke faruwa a Gaza, inda babban jami’i a tarayyar turai Josep Borrell yayi gargadin cewar “muna daf da fadawa cikin yaki tsundum.”

Amurka, ta sake yin jan kunne akan kaddamar da yaki ta kasa a Lebanon, inda wani babban jami’in Amurka ya sha alwashin samarda da dabarun da majalisar zata yi amfani dasu wajen magacnce kazancewar al\amura a makon da muke ciki.

Babu tabbas game da cigaban da za’a samu wajen sassauta wutar rikici a lebanon alhli duk kokarin da ake yi na tsagaita wuta a zirrin gaza, wanda isra’ila ke cigaba da kaiwa hare-hare babu kakkautawa tun wata oktoban bara, ya ci tura.