NAJERIYA: Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa Zai Nazarci Shirin Yakar Talauci

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da kwamitin da ke bashi shawara kan tattalin arziki, domin tattaunawa musamman akan rufe iyakokin kasar da makwabtanta, da kuma fasalin kudade wato Finance Act 2020, da yadda ya shafi haraji (VAT).

A hira ta musamman da Dr. Muhammad Sagagi mataimakin shugaban kwamitin da ke baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan tattalin arzikin kasa, ya ce yanzu kwamitin ya kai wata biyar kenan da kafuwa.

Ya ce cikin ayyukan da suka yi, na farko sun gana da ma'aikatan gwamnati daban daban kan irin ayyukan da suke yi, da kuma wandanda za su yi nan da shekaru hudu ko biyar masu zuwa.

Dr. Sagagi ya ce sun yi nazari akan wata magana da shugaban kasa yayi, ta cewa daga wannan shakara ta 2020, a kowacce shekara zai fidda a kalla mutum miliyan goma daga cikin talauci. Sun yi nazarin yadda shugaban kasa zai cika wannan alkawarin.

Ya sake cewa sun yi nazarin kan shirin da Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya take yi na rancen wasu kudade daga kasashen duniya daban daban, yadda wannan zai amfani kasa, da kuma fidda kasar daga wasu damuwa.

Dr Sagagi ya kuma kara da cewa, sun yi nazari kan rufe iyakokin Najeriya da makwabtanta, da halin da ake cikin, da dai sauransu.

Ya ce duk wannan sun yi ne domin shugaban kasa yana so ya ga yadda za a kara taimakawa al'ummar kasar, kuma sun yi nazari kan gyara da za a yi domin taimakawa ma'aikatu su yi aikin da zai amfani tattalin kasar.

A saurari hirar a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa:"Munyi Nazari Mun Baiwa Shugaban Kasa Shawara