Kwamitin Sulhu Na MDD Zai Zauna Asabar Din Nan Kan Rikicin Koriya Ta Arewa

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Amurka ta bukaci kwamitin sulhu ya amince da kudurin kakabawa Koriya ta Arewa Takunkumi.

Amurka tana neman kwamitin sulhu na MDD cikin hanzari ya amince kan wani kuduri da zai aza takunkumikan koriya ta Arewa. wanda zai hana kasar samun kudaden shiga har dala milyan dubu daya a shekara, kudade da take amfani da su wajen tafiyar shirin Nukiliya dana makamai masu linzami.

Yau Asabar ake sa ran kwamitin sulhun zai zauna kan wannan batu.

Daukar wannan mataki, yana a zaman martani ne kan gwajin makamai masu linzami masu cin dogon zango data kaddamar a ranakun 3 da kuma 28 ga watan jiya. Gwajin ya nuna yanzu kasar tana iya farwa Amurka da ma galibin kasashen turai.

Jakadu suka ce bayan da aka shafe makonni ana gudanar da shawarwari tsakanin Amurka da China, kwamitin sulhu zai jefa kuria da misalin karfe 3 na rana, watau misalin karfe 8 na dare agogon Najerya, da Nijar, kamaru d a cadi, watau bakwai na dare agogon Ghana.