Kwamitin Sulhu Na MDD Zaiyi Zaman Tattaunawa Kan Birnin Aleppo

Taron Kwamitin sulhu Na MDD

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya zaman tattaunawa na gaggawa a yau Laraba sakamakon karuwar tashe tsahen hankula a Birnin Aleppo dake Arewacin Syria.

Birtaniya da Faransa sunyi kiran wannan zama ne wanda Jakadan Rasha a Majalisar dinkin duniya Viatly Churkin ya soka a matsayin “Kamfe na farfaganda”.

Ya biyo bayan tsattsauran hasashen a ranar Talata daga tawagar MDD daga Syria, Staffan De Mistura na yakin da ake a Aleppo yana kara zafi sannan Fararen hula na famar tserewa.

Wata kungiyar Rajin kare hakin dana dam dake Sa ido a Syria, wacce ke da mazauni a Birtaniya, ta bada rahoton kusan mutane dubu 50,000 ne suka tsere Gabashin Aleppo a kwanaki hudu da suka wuce.

Karuwar tashin hankalin ta tilasta wa fararen hula da su gudu su bar gidajen su batare da daukan komai a hannunsu ba, Lamarin da Shugaban Kungiyar Rajin Dan adam ta MDD Stephen O’Brien ya bayyana da “abin lura da kuma tsoratarwa.”