A jiya Litnin ne aka sami amincewar wannan kudurin da ya janyo murda gashin baki sosai a tsakanin kasashe 15 dake kan wannan kwamitin na tsaro, inda aka ga Rasha da China suna ta anfani da kuri’unsu na hawan kujerar naki gameda wannan matakin da ake ganin kasashen yammaci na son dauka don sawwaka wahalolin da mutanen na Aleppo ke sha.
Haka kuma zancen na tasowa ne a daidai lokacinda aka soma aikin kwasar dubban mutane daga Aleppon, bayanda aka jinkirta aikin a sanadin tashe-tashen bama-bammai da harbe-harbe a tsakanin rukunonin dake adawa da juna.
Ministan harakokin wajen Turkiya, Melvut Cavusoglu yace izuwa da marecen Litnin, an riga an kwashe mutane kamar dubu 20 daga Aleppo din, an fice da su.
Sai dai har yanzu akwai wasu dubbai da suka rage cikin Aleppo din, garinda ‘yantawaye suka kwace shi tun shekarar 2012, a matsayin daya daga cikin matakan da suka dauka na neman ganin bayan gwamnatin shugaban Syria din, Bashar al-Assad.