Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, a jiya Alhamis ya sake sabunta kudirin sa na samar da zanman lafiya a Sudan ta Kudu har na wani tsawon shekara gudatare da barazanan sawa kasar takunkumi game da makamai muddin dai aka ci gaba da fada.
Kudirin wanda Amurka ce ta aike dashi wajen taron ta bayyana cewakwamitin na duba yiwuwar daukar dukkan matakan da suka dace akan duk wasu masu kokarin kawo wa zaman lafiya da tsaro cikas a kasar ta Sudan ta Kudu.
Tace tana ganin dakatar da sayar da makamai da shiga dasu cikin kasar zai durkusad da sassan biyu masu fada da juna.
A cikin shekarar 2011 ne Kasar ta Sudan ta Kudu ta samu yancin ta daga Kasar Sudan, amma kuma tun daga wannan lokacin yakin basasa ya barke tsakanin sassa biyu, wato tsakanin bangaren shugaban kasa Salva Kiir da mataimakin shugaban kasa Riek Machar.
Ko a cikin watan disamban bara an sa hannu akan samar da zaman lafiya amma hakan bai yi nasara ba.
Yanzu haka dai kasar tana fama da matsanancin rashin abinci, domin an kiyasta cewa mutane da suka kai miliyan 4 sun bar kasar da yaki, talauci, don tsananin yunwa data addabe su
Wannan yasa kasar ta zama kasar dake kan gaba a duk fadin duniya da yan gudun hijiran suka fi kowa zama cikin matsanancin damuwa.
Wani kwararre a harkan kare hakkin bil adama na MDD yace a kalla jami’an gwamnatin kasar da sojoji sama da 40 ne yanzu haka suke fuskantar tuhuma akan aikata ba dai-dai ba ga al’umma.