Kwamitin Sulhu Na MDD Na Yunkurin Ziyartar Kabilar Rohyngya A Bangladesh

Gustavo Meza-Cuadra, shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD

Idan kwamitin sulhun ya kai ziyara Bamgladesh da Myanmar zai ga halin da 'yan kabilar Rohyngya musulmi ke ciki wadanda fiye da dubu dari bakwai na gudun hijira a Banglaesh din biyo bayan kashe kashen da sojojin Myanmar suka yi masu a kasarsu

Watakil wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, su kai ziyara kasashen Myanmar da Bangladsh cikin watan nan domin gane ma kansu halin da dubban musulmi 'yan kabilar Rohyngya suke ciki wadanda suka gudu daga matakan murkushesu da sojojin Myanmar suke yi.

"Yanzu dai muna shirya sharudda da ka'idoji, inji shugaban kwamitin na wannan wata, jakadan kasar Peru Gustavo Meza-Cuadra ya gayawa manema labarai jiya Litinin.

Kimanin tsiraru musulmi 'yan kabilar Rohyingya su dubu dari bakwai ne suka gudu daga jahar Rakhine zuwa makwbciyar kasa Bangladesh tun watan Agustan bara, bayan harin da mayakan sakai 'yan kabilar suka kaiwa dakarun kasar hari, martanin harin ne jami'an tsaron kasar suka dauka, har MDD tace an shirya gayyar da tsari, wadda ya tafi dai dai da ma'anar abunda litattafai suka wallafa kan abunda ake kira 'kisan kare dangi" ko kawar da wata kabila baki daya daga wani wuri.

Sai dai jakada Meza yaki ya bada wani karin bayani, illa kurum cewa ya yi har yanzu suna aiki kan wannan ziyara.