Anyi Kira Ga Kasashen Duniya Su Yanke Hulda Da Kasar Myanmar

Kwamitin binciken kut da kut na MDD, na kiran kasashen duniya da su yanke hurdar dake tsakanin su da hukumomin sojan kasar Myanmar

Wani Kwamitin musamman mai binciken kut da kut na Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci kasashen duniya da su yanke huldar dake tsakanin su da hukumomin sojan kasar Myanmar, a wani yunkuri na ganin sun daina gallazawa tsirarun Musulmai na kabilar Rohingya.

A can baya, tun a watan Ogusta na shekarar 2017, kwamitin na musamman ya taba zargin sojojin da cin zarafin Musulmai na Rohingya, inda suka rinka nuna musu wulakanci da yi musu kisan gilla.

Fiye da mutane dubu 700 ne, ‘yan kabilar Rohingya suka yi gudun hijira daga jihar Rakhine, zuwa kasar Bangladesh, don gujewa gallazawar da ake musu.

A hirraraki daban-daban da aka yi da daruruwan su, ‘yan jinsin Rohingya din sunce, cin zarafin su da ake musu, ya hada da yi musu fyade, kisan gilla, da kona kauyukkansu.