Mataimakin Kakakin Majalisar Benjamin Kalu wanda ya jagoranci zaman majalisar na yau Alhamis ne ya karanta wasikar da ta fito daga kwamitin da ke dauke da sunayen jihohin da aka ba da shawarar kirkirar.
Washington dc —
Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya akan gyaran kundin tsarin mulkin 1999 ya bada shawarar kirkirar karin jihohi 31 a kasar.
Mataimakin Kakakin Majalisar Benjamin Kalu wanda ya jagoranci zaman majalisar na yau Alhamis ne ya karanta wasikar da ta fito daga kwamitin da ke dauke da sunayen jihohin da aka ba da shawarar kirkirar.
Idan har aka amince da shawarar, hakan zai kara adadin jihohin Najeriya zuwa 67.
An ruwaito wasikar na cewar: “ana sanar da mambobin kwamitin Majalisar Wakilai akan gyaran kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na, 1999 (da aka yiwa kwaskwarima), an karbi shawarwarin majalisa akan kirkirar jihohi da kananan hukumomi.