Majalisar dokokin Taraba ta kafa kwamitin jin bahasin jama'a akan dokar da ta hana kiwo a jihar da gwamnan ya gabatarwa majalisar wadda kuma ta jawo cecekuce musamman ma tsakanin Fulani da dokar zata fi shafa
Kwamitin majalisar dokokin jihar ya fara zaman jinbahasin jama’a amma hadakar kungiyoyin Fulani hadakar sun kauracewa zaman kwamitin .
Majalisar dokokin jihar Taraban dai ta tsara shirya jin bahasin jama’a ne game da kudirin dokar haramatawa makiyaya kiwo a fadin jihar baki daya a shiyyoyi uku na majalisar dattawan jihar.
Tun farko dai shugaban kwamitin Mr Mark Useni yace kwamitin zai yi zamansa a wurare uku,inda zai fara da Jalingo dake yankin shiyar Taraba ta arewa inda za’a yi kwana biyu,daga nan kuma sai shiyar Wukari da za’a soma a gobe alhamsi daga nan kuma sai a kammala da shiyar Taraba ta tsakiya inda kwamitin zai yi zaman kwanaki biyu a garin Bali wato daga ranar takwas ga wannan wata na Yuli.
To sai dai tun ba’a je ko ina ba,kungiyoyin Fulani a ciki dama wajen jihar suka yi tir da zaman kwamitin. Koda yake kaddamar da zaman kwamitin a garin Jalingo,kakakin majalisar dokokin jihar Abel Peter Diah,yace zasu cigaba da wannan zama.
‘’Duk da cewa wasu na korafi, za’a cigaba da zama, don jin ra’ayin jama’a. Kama daga masu goyon baya da kuma wadanda basa goyon baya,don haka ne kawai za’a baiwa kowa yancinsa", inji kakakin majalisar.
,’Mai girma gwamnan jiha ne dai ya kawo wannan kudirin doka don magance tashe tashen hankulan dake aukuwa a tsakanin makiyaya da manoma a jihar’ a cewar kakakin majalisar dokokin jihar Taraban.
To sai dai yayin da kwamitin ke fara zama, hadakar kungiyoyin Fulani da Makiyaya sun kauracewa zaman kwamitin bisa abun da suka kira rashin tausaya wa game da irin asarar rayukan da aka yi a tsaunin Mambilla cikin kwanakin nan.
A wajen taron manema labarai don kauracewar,shugabanin kungiyar makiyayan sun yi zargin cewa da wata manufa aka ma soma ma zama, ganin irin rayukan da suka salwanta to amma 'yan majalisar ko tir basu yi ba, amma kwamiti zai yi zama,saboda haka suka bukaci gwamnatin tarayya da ta shigo ciki game da abubuwan dake faruwa a jihar.
Da farko dai shugaban kungiyar Fulani Ta Korel Inuwa Sa’idu yace basu yarda ba. Ita ma dai uwar kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, ta nuna takaicinta game da matakin soma jin bahasin jama’a da yan majalisar suka soma,musamman a wannan lokaci da ake alhini.
Mafindi Umaru Danburam dake zama mataimakin shugaban kungiyar,mai kula da jihohin arewa maso gabas ya mika kokon baransu ne ga gwamnatin tarayya.
Ga karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz:
Your browser doesn’t support HTML5