Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Kira Ga Kasar Burundi

Burundi

Kwamitin yaki da cin zarafi da kuntatawa na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwar sa akan rahoton da ke cewa wasu Lauyoyi 4 ‘yan kasar Burundi suna huskantar kwace lasisin su na gudanar da aikin lauya domin kawai sun baiwa kwamitin wasu bayanai.

A cikin wata sanarwan da kwamitin ya fitar jiya litini ya bukaci gwamnatin kasar ta Burundi data bada tabbacin cewa ba wani lauya da zai huskanci hukuba domin kawai ya baiwa kwamitin hadin kan da yake bukata.

Kwamitin yace lauyoyin da wannan abu ya shafa ko sun hada da Armel Niyongere, Lambert Nigarura,Dieudonne Bashirahishize, sai Vital Nshimirimana.

Wadannan dai sune suka tainmaka wa rahoton da kungiyoyi masu zaman kansu na kasar ta Burundi da kwamitin ta MDD ta samu tattara bayanai kuntatawa jamaa da akayi a kasar.

Biyo bayan wannan gudun mowar da suka bayar ne sai babban mai gabatar da kara na kasar ya bukaci shugaban Lauyoyin kasar da ya hana su damar ci gaba da gudanar da ayyukan su na lauyoyi masu zaman kansu, tare da musu kazafin aikata wasu munanan ayyuka, ciki ko harda yunkurin juyin mulki.

Haka kuma a ranar da aka aiwatar da wadannan danyen aikin ga wadannan lauyoyin ne kwaran kuma sai ga gwamnatin kasar tace ba zata ci gaba da zaman tattaunawar da kwamitin ba.