Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar UNFPA Ta Majalisar Dinkin Duniya Ta Janye Tallafin Haihuwa a Nijar


Tambarin Hukumar UNFPA Ta Majalisar Dinkin Duniya
Tambarin Hukumar UNFPA Ta Majalisar Dinkin Duniya

Hukumar ta UNFPA da ke taimakawa mata masu haihuwa a Nijar bisa zuwa asibiti a kyauta na tsawon lokaci a kasar, ta janye tallafin na taimakawa waje rage mace-macen mata da yara wajen haihuwa.

An dauki tsawon lokaci a Jamhuriyar Nijar wajen kulawa da kuma bada magani kyauta ga mata masu juna biyu, musamman a lokacin haihuwarsu, don rage mace-macen da hakan ke haddasawa.

To kwatsam sai ga labarin soke wannan tallafi da suke samu daga wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya. Mutanen Jamhuriyar ta Nijar sun bayyana tashin hankalinsu matuka game da janye wannan tallafi da ya dau tsawon shekaru ana yi.

Wasu mazauna kasar sun yi kira ga gwamantinsu da ta yi duk mai yiwuwa wajen nemo wani sabon tallafin daga ko ma ina za a iya samunsa a duniya domin ci gaba da wannan aikin ceton rayukan masu dauke da juna biyu.

Wakilinmu a Nijar Haruna Mamman Bako ne ya aiko mana da wannan rahoton da yake manne a makalar kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG