Kwamitin Gyara Dokokin Zabe Ya Isa Arewa ta Tsakiya

Kwamitin gyara dokokin zaben Najeriya a karkashin shugabancin Sanata Ken Nnamani wanda yake zaune ta hagu

Kwamitin gyara dokokin zaben Najeriya da Shugaba Muhammad Buhari ya kafa a karkashin jagorancin tsohon kakakin majalisar dattawa Sanata Ken Nnemani, ya gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'ar jihohin arewa ta tsakiya a Jos, babban birnin Filato.

Shugaban kwamitin Sanata Ken Nnamani ya bayyana cewa manufar kwamitin shi ne ya tattara ra'ayoyin jama'a domin samun masalaha da kaucewa matsalolin zabe da suka hada da rashin kammala zabe, tashin hankali bayan zaben da rawar da hukumar zabe zata taka lokacin fidda 'yan takara domin a samu zabe mai inganci a kasar.

Shugaban ya cigaba da cewa mafi yawan koke-koken da kotunan zabe ke samu shi ne na yin magudi musamman yayin fitar da 'yan takara. Yace suna neman ra'ayoyin jama'a kan ko hukumar zabe zata sa ido a zaben fidda gwani da jam'iyyu ke gudanarwa har ta iya dakatar da wanda ba shi ne jama'a suka zaba ba.

Kwamitin gyara dokokin zabe da Sanata Ken Nnamani ke jagora

Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong yace yanada yakinin gwamnati zata aiwatar da rahoton da kwamitin zai bayar. Yace ko a kungiyar gwamnoni ma sun rubuta nasu ra'ayoyin sun mikawa kwamitin.

Dangane da cewa su 'yan siyasa suke haddasa rikici lokaci ko bayan zabe, Gwamna Lalong yace bisa ga dokokin ne. Idan akwai dokoki yana da kyau ana binsu sau da kafa kuma duk wanda ya karyasu a yi masa hukumcin da doka ta tanada. Amma ana gani inda mutum ya hada rikici wurin zabe kuma ba'a yi masa hukumci ba. Ya roka a cikin gyaran a sa dokar da zata yiwa mutum hukumci idan ya saba mata. Ko wakilin zabe ya sabawa doka shi ma a hukumtashi.

Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Ibrahim Balarabe Abdullahi yace sun gabatar da nasu kudurin wa kwamitin. Yace a duba dokokin zabe gaba daya yadda talakawa zasu ji dadi.

Wasu masu ruwa da tsaki a harkokin zabe sun bayyana nasu ra'ayoyin. Wani da ya tsaya takarar kujerar gwamnan Filato yace abun da ya fi haddasa rikici shi ne kawo wani daban a dorashi dole kan sauran 'yan takara a ce shi ne zai tsaya saboda wani ubangidansa ko wani jigo a jam'iyyarsa.Idan an bar wadanda suke siyasar su fafata su tsayar da dan takara to ba za a samu matsala ba.

Wata cewa tayi a rage shekarun tsayawa zabe. A bar dan shekara talatin ya nemi shugabancin kasa saboda matashi ne yana da karfin aiki kuma 'yan kasar na iya tambayarsa dalilin da ya sa bai yi wasu abubuwa ba idan ta kama a yi hakan.

Taron na Jos shi ne na jin ra'ayoyin al'ummar jihohin arewa ta tsakiya.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamitin Gyaran Dokokin Zabe Ya Isa Arewa ta Tsakiya - 4' 04"