Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Najeriya INEC Ta Fitar da Jadawalin Zaben 2019


Nick Dazan daraktan labarai da hulda da jama'a na hukumar zaben Najeriya INEC
Nick Dazan daraktan labarai da hulda da jama'a na hukumar zaben Najeriya INEC

Hukumar zaben Najeriya wato INEC ta fitar da jadawalin zaben shekarar 2019 kamar yadda daraktan bada labaran hukumar Nick Dazan ya shaidawa Muryar Amurka

Yace yau hukumar zabe tayi nazari akan zabukan da zata aiwatar a shekarar 2019 kuma ta fitar da jidawalin zabukan.

Za'a yi zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya zanar Asabar 16 ga watan Fabrarirun shekarar 2019.

Zaben gwamnoni zai biyo baya da na majalisun jihohi da kananan hukumomi da birnin tarayya ranar Asabar 2 ga watan Maris na shekarar

Baicin kwanakin hutu Nick Dazan yace kusan kwanaki dari biyar ne suka rage kafin a soma zabukan, saboda haka wajibi ne a fitar da jadawalin cikin lokaci yadda kowa zai fahimci hankinsa musamman masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da zabe.

Inji Nick Dazan dama dokar kasa da ta hukumar zaben sun tanadi cewa a fitar da jadawalin zabuka fiye da shekara daya kafin a gudanar dasu saboda kowa ya san abun da shirin ya kumsa da abubuwan da yakamata masu sha'awar shiga takara su san abun da zasu yi.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG