Shugaban kwamitin binciken Yusuf Shehu Musa shi ya bayyana a bainar jama'a yin watsi da zarge-zargen goma sha shida.
Shugaban yace sun dauki matakin ne domin 'yan majalisar sun kasa bada shaidar da zata tabbatar da zargin da suke yi. Yusuf Shehu Musa yace kwamitin zai gabatar da rahotonsa ga majalisa kamar yadda doka ta tanada.
A cikin garin Lafiya babban birnin jihar mutane sun fadi albarkacin bakinsu game da abun da kwamitin yayi. Tsohon shugaban karamar hukumar Doma yace hukuncin kwamitin yayi masu dadi domin ya wanke gwamnan. Amma wani Yakubu Muhammed wanda shi ma ya taba rike mukamin shugaban karamar hukuma yace dokar kasa ta hana a sa jami'in gwamnati ko wani mai karbar albashin gwamnati ya kasance cikin kwamitin. Yace tun da ba'a bi ka'ida ba wurin nada kwamitin to a wurin 'yan majalisa babu kwamiti ke nan.
Muhammed Barde Agwai shugaban matasan PDP yace abun ya zama tamkar wasan yara ne domin 'yan kwamitin din ba alkalai ba ne. Ba'a ce su yi shari'a ba. Bincike aka ce su yi. Bayan binciken su fadi abun da suka gani a rubuce su mikawa majalisa. Tun da basu yi haka ba zamansu ya zama haram kuma abun da suka yi haram ne.
Gwamna Tanko Almakura kuwa godiya ya yiwa Allah. Yace 'yan majalisa su ashirin 'yan PDP sun nemi su yi masa kage su ci masa mutunci su kuma fake da yawansu a majalisa domin su tsigeshi amma Allah bai yadda ba. Nasarar da ya samu ba tashi kadai ba ce. Nasara ce ta dimokradiya. Ya kira jama'a su bi gaskiya su bi doka.
Shi kuma shugaban kwamitin na majalisar jihar Muhammed Baba Ibako yace su basu san kwamitin binciken ba. Suna da matakin da zasu dauka kuma zasu fadawa Najeriya abun da zasu yi. Yace su ba zasu je kotu ba. Sun gama aikinsu wadanda basu gamsu ba su ne zasu iya zuwa kotu. Dangane da cewa kwamitin zai kawo masu rahoto yace suna jira.
Wani lauya Hassan Liman yace hukuncin da aka yanke an bi ka'ida. Yin watsi da karar na bisa hanya.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5