Kwamitin Binciken Majalisar Wakilan Amurka Na Cigaba Da Shirin Binciken Yiwuwar Tsige Trump.

Jami’an diflomasiyya na yanzu da na baya da kuma jami’an tsaron kasa sun riga sun ba da ba'asi a sirrance a ‘yan makonnin da suka gabata.

‘Yan kwamitin binciken sirrin majalisar wakilan Amurka na yin shirye-shiryen su na karshe don sauraron ba'asi karon farko a bainar jama'a akan binciken yiwuwar tsige Shugaba Donald Trump.

Cikin Shaidun da za su bada bahasi gobe Laraba akwai William Taylor, shugaban ofishin jakadancin Amurka a Ukraine, da George Kent, Mataimakin Sakataren da ke kula da Ofishin Tarayyar Turai da kuma wasu kasashen yankin Asiya.

Duka mutanen biyu, Taylor da Kent suna daga cikin jami’an diflomasiyya na yanzu da na baya da kuma jami’an tsaron kasa da suka riga suka ba da ba'asi a kebance a ‘yan makonnin da suka gabata.

Kwamitocin majalisar wakilan sun fidda rubutaccen bayanan da jami’an su ka yi inda suka ba da cikakken bayani akan yadda Trump da hadimansa suka hura wa Ukraine wuta akan ta kaddamar da bincike akan daya daga cikin babban ‘yan adawar Trump a zaben shekarar 2020 daga jam’iyyar Democrat, wato tsohon Mataimakin Shugaban kasa Joe Biden, da dansa Hunter Biden musamman akan ayyukan da suka yi a wani kamfanin gas din Ukraine da kuma wani batu mara tushe mai cewa Ukraine ta yi katsalanda a zaben shekarar 2016, ba Rasha ba, kamar yadda hukumar binciken sirrin Amurka ta fada.