An lika takardun gayyatan ne a kofar shiga gidan gwamnati dake Yola. An bukacesu da su bayyana a gaban kwamitin gobe Jumma'a.
A takardar gayyatar ta gwamna an bayyana masa lokacin da zai bayyana da wurin da zai bayyana, amma takardar mataimakinsa bata bayyana lokaci ko wurin da ake son ya bayyana ba sadai ranar.
To saidai inda 'yan kwamitin ke yin taronsu ba'a bari kowa ya shiga ba hatta 'yan jarida. Kamar yadda ake zato tuni lamarin ya soma kawo cecekuce. Ibrahim Baffa Waziri wani tsohon dan majalisar Adamawan yace akwai abun dubawa a batun.
Rashin bayyana inda mataimakin gwamnan zai bayyana a gaban kwamitin ya kawo daurin kai. Haka kuma da can majalisa ta bada umurni a fara binciken mataimakin gwamna tukunna kafina a kawo kan gwamnan amma sai gashi za'a fara da gwamnan.
A wani halin kuma sarakuna da shugabannin addini sun yi taruka inda suke bukatan gwamnan da 'yan majalisar su sasanta domin tuni dambarwar ta jefa al'ummar jihar cikin wani mawuyacin hali.
Shugaban kungiyar IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau yace su basu goyi bayan tsige gwamnan da mataimkinsa a wannan lokacin ba. Shi ma Rev Isa Aruwa yace dole ne a yi takatsantsan ganin irin halin da jihar ke ciki. Yace cire gwamna yanzu ba zai kawowa jihar alheri ba. Maimakon haka cireshi zai sake saka jihar cikin wani rudani.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5