Kwamitin Ayyukan Leken Asirin Majalisar Dokokin Amurka Ta Fitar Da kasidar Sirri

Devin Nunes,

Kwamitin ayyukan leken asiri na Majalisar wakilan Amurka ya fitar da kasidar sirri inda aka bayyana zargin da 'yan jam'iyar Republican a majalisa suka yi cewa, masu gudanar da bincike na hukumar binciken manyan laifuka ta FBI sun sabawa doka a binciken katsalandan da ake zargi Rasha a kai

Jiya Jumma'a aka fitar da kasidar sirrin, jim kadan bayanda shugaba Donald Trump ya amince a fitar da kasidar da shugaban kwamitin leken asirin dan jam'iyar Republican Devin Nunes ya rubuta.

Shafunan da dama na kasidar sun maida hankali kan tsarin leken asiri dake sa ido kan wadansu a kasashen ketare da ake kira (FISA) izinin da ya ba hukumar FBI damar sa ido kan tsohon mai ba shugaba Donald Trump shawarwari kan harkokin kasashen ketare Carter Page, wani dan kasuwa dake da jari a Russia.

Ana bayyana damuwa dangane da zargin da ake yi cewa Page ya yi hulda da jami'an leken asirin kasar Russia

Kasidar sirrin ta nuna cewa, bayanan da tsohon dan leken asiri Christopher Steele ya tattara sune aka bada karfi a kai wajen neman izinin amfani da FISA a wajen sawa Page ido, yayind hukumar FBI kuma bata bayyana cewa ofishin yakin neman zabe na Hillary Clinton wadda take takara a lokacin, da kuma ofishin jam'iyar Democrat na kasa suka dauki nauyin binciken da Steele ya gudanar ba, ko kuma cewa Steel ya taba bayyana kin jinin Trump a lokutan baya.