Kwamitin musamman na wakilan majalisar dokokin Amurka da aka azawa alhakin rage gibi a kasafin kudin Amurka na dala miliyan zambar da dubun dari biyu ya gaza cimma yarjejeniya.
Shugabannin kwamitin hadin guiwar biyu ne suka bayyana haka jiya litinin. Wakilan kwamitin suka ce “kodashike mun gaza cimma daidaito kan batutuwa da suka raba mu, zamu dasa aya da cewa baki yazo daya, kuma mun hakikance cewa tilas ne mu tunkari matsalar kudi da kasarmu take fuskanta, kuma ayi wani abu a kai, ba lamari ne da zamu barwa masu tasowa su warware ba.”
Daga bisani a daren jiya shugaban Amurka Barack Obama yayi barazanar zai hau kujerar naki kan duk wani yunkuri na neman tada alkawarin zabtare kudade daga sassa daban daban da aka shar’anta cikin dokar kasafin kudi.