Kwale-Kwale Ya Kife Da Mutane Sama Da 46 A  Zamfara

Zamfara_kwale-kwale

Kantoman karamar hukumar Bukkuyum, Nasiru Muhammad, wanda ya ba da tabbacin faruwar lamarin yace, an samu hatsarin ne saboda lodi fiye da kima, da rashin hakuri.

A wani mummunan hatsari a jihar Zamfara, wani kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji 46 ya kife a garin Bukkuyum Mashayar Garba Rogo da ke karamar hukumar Bukkuyum a safiyar yau Talata.

Kantoman karamar hukumar Bukkuyum, Nasiru Muhammad, wanda ya ba da tabbacin faruwar lamarin yace, an samu hatsarin ne saboda lodin wuce kima, da rashin hakuri a jira layin jigilar mutane zuwa gonakin su.

“Mun yi zama da masu aikin fito na jirgin ruwa, za mu dauki matakai don kai karshen matsalar. Yanzu muna da wasu a asibiti daga cikin wadanda abun ya shafa. Lamarin bai yi dadi ba sam.” Inji kantoman

Asibiti

A cewar Malam Aliyu Umar Bukkuyum, wani mazaunin yankin, kwale-kwalen ya kife ne da misalin karfe 10:30 na safe.

Yara hudu ne suka nutse a cikin hatsarin, inda aka tsinto gawawwaki biyu yayin da sauran suka bace. An ceto wasu 12 kuma a halin yanzu suna samun kulawa a babban asibitin Bukkuyum.

Asibiti

Wani da ya tsira, Buhari Usman (wanda ake yi wa lakabi da Messi), ya ba da labarin irin halin da ya shiga. Ya tabbatar da cewa kimanin fasinjoji 50 ne akasari yara da wasu manya ne ke cikin kwale-kwalen da ke kan hanyarsu zuwa gonakinsu.

Asibiti

Sai dai kuma ana tsakiyar tafiya kwale-kwalen ya fara tangal - tangal da ba a saba gani ba, kuma duk da kokarin da masu aikin jirgin suka yi, sai ya kife.

“Ni da kaina na ceci yara 12 da wasu manya. An ceto da yawa, amma abin takaici, yara huɗu sun mutu. An gano gawawwaki biyu, biyu kuma ba a gansu ba,” inji Buhari.

Ku Duba Wannan Ma An Ceto Mutane 5, Tare Da Gano Gawawwaki 9 Daga Hatsarin Kwale-Kwalen Zamfara
Ku Duba Wannan Ma Mutane 35 Sun Bace Cikin Ruwa A Zamfara

Wannan dai shi ne iftila'in kwale-kwale na uku biyo bayan kifewar wasu kwale-kwalen guda biyu da aka yi a karamar hukumar Gummi a baya-bayan nan, inda wani hatsarin ya rutsa da fasinjoji sama da 40 da kuma wani a Nasarawar Kifi, inda wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 30 kuma ya kife.

~Abdulrazak Bello~