Kwalara Ta Kashe Mutane 25 A Sokoto

Cholera

Kwamishinan lafiya ta jihar, Hajiya Asabe Balarabe wacce ta bayyana hakan ga manema labarai a Sokoto, tace a halin yanzu jihar na bada kulawa ga mutane 15 da suka kamu da cutar.

Akalla mutane 25 ne suka mutu sannan wasu da dama na samun kulawa a asibiti sakamakon barkewar annobar kwalara a kananan hukumomin jihar sokoto 3 da suka hada da; Sokoto ta Arewa da Silame da Kware.

Kwamishinan lafiya ta jihar, Hajiya Asabe Balarabe wacce ta bayyana hakan ga manema labarai a Sokoto, tace a halin yanzu jihar na bada kulawa ga mutane 15 da suka kamu da cutar.

A cewarta, an gano cewa mutanen 15 sun kamu da cutar ne bayan gwaje-gwajen likitoci sun tabbatar cewa annobar kwalara ce.

Ta kara da cewa ana zargin mutane 1, 160 sun kamu da cutar kuma 25 daga cikin su sun rigamu gidan gaskiya.

A cewarta, kungiyoyin bada agaji na aiki tare da gwamnatin jihar wajen dakile yaduwar muguwar cutar.