Kurdawan Syria Sun Taya Zababben Shugaba Joe Biden Murnar Lashe Zabe

Shugabannin Kurdawa na Syria na bayyana kwarin gwiwa kan ci gaban goyon bayan Amurka ga dakarunsu biyo bayan nasarar da tsohon mataimakin Shugaba Joe Biden ya samu a zaben shugaban kasa na Amurka a makon da ya gabata.

Dakarun SDF da kurdawa ke jagoranta manyan abokan huldar Amurka ne a yakin da suke yi da kungiyar ‘yan ta’addana IS. Tare da goyon bayan dakarun kasa-da-kasa da Amurka ke jagoranta a yakin da ‘yan IS, dakarun SDF suka ‘yantar da yawancin yankunan da a baya ke hannun mayakan IS a Syria.

Mazloum Abdi, kwamanda-Janar din dakarun SDF, ya taya zababben shugaba Joe Biden murna da mataimakiyarsa Kamala Harris akan nasarar zaben da suka samu.

Biyo bayan janye wasu dakarun Amurka daga arewa maso gabashin Syria a watan Oktoban shekarar 2019 da kuma mamayar da Turkiyya ta yi a yankin daga baya, ya haifar da fargaba tsakanin al’ummomin kurdawa a Syria kan cewa Amurka zata yi watsi da su gaba daya.