Sakataren Tsaron Amurka, Mark Esper, ya ce Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne "ke da cikakken alhakin" farfadowar kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS, da halin kakanikayi da jama’a suka shiga, da kuma yiwuwar aikata laifukan yaki.
Wannan ita ce zazzafar suka ko kuma Allah wadai da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi kan matakin soji da Turkiyya ta dauka akan mayakan Kurdawa a arewacin Siriya.
Esper ya kira harin da Turkiyya ta kai wa Kurdawan "marar ma’ana da babu hange a ciki."
Ya kuma ce matakin ya maido da hannun agogo baya kan abin da ya kira “nasarar da gamayyar dakarun kasashen duniya suka samu wajen kakkabe kungiyar ISIS a Syria, lamarin da ya ce zai bai wa muggan mayakan ISIS damar tserewa daga sansanonin da Kurdawa ke tsare da su.
Sakataren tsaron Amurkan har ila yau ya ce, dangantakar Amurka da Turkiyya za ta raunana sanadiyyar wannan hari, yana mai cewa zai je birnin Brussels a mako mai zuwa don nuna matsin lamba ga sauran mambobin kungiyar tsaro ta NATO da nufin su sanyawa Turkiyya takunkumi.
A makon da ya gabata ne, sojojin Turkiyya suka shiga arewacin Siriya bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin janye sojojin kasarsa kusan 1,000, daga yankin, inda za a sake tura su wasu yankuna a Gabas ta Tsakiya, don su "sa ido kan lamarin,” kamar yadda Trump ya fada.