Rikincin dai yayi sanadiyar asarar rayuka da kuma jikkata wasu da yawa kamar yadda babban limamin Masallacin Juma’a na garin Aba Mallam Idris ya fada, inda yace “ba wani bahaushe dake da hannu, tunda kamar yadda muka sami tabbacin abinda ya faru tsakanin sojane da wasu mashaya inda suka buge shi, shikuma ya dauko abokansa suka kama wadannan yaran, daga kuma suka farma Hausawa da kisa.”
A cewar Mallam Idris, yanzu haka dai mutane biyar ne suka rasa rayukansu, wasu da dama kuma sun raunata. Har yanzu dai akwai zaman dar dar a garin inda Dubban Hausawa ke fakewa a babban Masallaci, yayin da jami’an tsaro ke iyaka bakin kokarinsu don maido da zaman lafiya.
Rundunar Yan Sandan jihar Abia, ta tabbatar da afkuwar lamarin inda take nuni da cewa mutane uku ne kadai suka rasa rayukansu, tare da wasu da dama da suka jikkata.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5