Tuni dai aka rattaba hannu kan wadansu muhimman yarjeniyoyi da kasashen biyu ke ganin idan aka aiwatar da su, sha’anonin dake gabansu zasu inganta ta farkin tsaro da fannin ninikayya da kuma bunkasa tattalin arziki.
Kakakin shugaba Mohammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, yayi karin haske kan wannan batutuwan da jarjejeniyar ta tabo a karshen ziyarar kwanaki biyu da shugaban Kamaru ya kai Najeriya.
Mallam Garba Shehu yace, “an jaddada yarjejeniya tsakanin Najeriya cewa su karfafa tsaro, saboda ana ganin riba da amfani zuwa yanzu ga irin hadin kan da aka samu. Sai kuma maganar iyaka da Majalisar Dinkin duniya ke zanawa tsakanin Najeriya da Kamaru wanda yake abune mai wuya kuma yana daukar lokaci, sai dai anyi hakuri an kai zuciya nesa in ba haka ba sai rai ya baci.”
Ya ci gaba da cewa anyi wata jarjejeniya musamman kan yan kasuwar Kamaru da Najeriya, domin a baya anayin ciniki ne kawai ba tare da sa hannun gwamnati ba, yanzu kuwa za a kafa musu wani zaure nasu wanda zasu ringa zama suna yin taro a Abuja.
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.