Kungoyoyin Siyasa Na Bukatar A Cire Shugaban INEC Ko Su Shiga Zanga-Zanga

Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta

A Yayin Zabukan gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a fadin Najeriya, wasu kungiyoyi sun bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori shugaban hukumar zaben Najeriya bisa zarginsa da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa ba bisa ka’ida ba, ko kuma matasan kasar su shiga zanga-zanga.

Shugaban kungiyar Injiniya Daniel Balarabe Gambo ne yayi wannan kiran a yayin hira da manema labarai a Abuja.

Tun bayan ayyana wanda ya ci shugaban kasa a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga wantan Fabrairu, jam’iyyun adawa ke ci gaba da nuna rashin amincewar su tare da shan alwashin zuwa kotu don bin kadi.

Sati biyu bayan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya jagoranci zanga-zanga zuwa babban ofishin INEC a Abuja, wata kungiya mai goyon bayan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour ta ce cire shugaban hukumar zabe ne kadai zai sa ba zasu shiga zanga-zanga a fadin jihohin kasar ba.

A nasa bangaren masanin shari’a Barrista Abdulhamid Mohammed SAN, a hirar sa da wakilin Muryar Amurka Alhassan Bala, ya ce zanga-zanga ba ita ce mafita ba.

Su kuma masana harkokin siyasa irin su Farfesa Ghali Sadiq na jami’ar Abuja, ya ce hukumar zaben tayi kura-kurai amma zanga-zanga ba zata haifar da da mai ido ba.