Yanzu haka kungiyoyin ma’aikata da masana sun fara maida martani na yadda yakamata ayi, domin kawo yanzu akwai wasu sama da Naira biliyan uku da ake zargin wasu gwamnoni da rashin bin ka'ida da tsare-tsaren da aka basu na yadda za su yi amfani da kason farko.
Ana zargin cewa gwamnonin sun yi abun da suka ga dama da kudaden ko da yake gwamnati ba ta bayyana sunayen jihohin da suka yi gaban kansu da kudin ba.
A farkon makon nan ne Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya ba ministar kudi da gwamnan babban bankin kasar umurnin sakarwa jihohi Naira Biliyan 500, cikin gaggawa. Kudaden na cikin rarar da aka samo daga kungiyar Paris Club, da ta mayarwa Najeriya saboda ta biya fiye da bashin da kungiyar ke binta.
Sai dai yayin da ake shirin raba masu kudaden, akwai wasu sama da Naira Biliyan uku da ake zargin wasu gwamnoni da rashin bin ka'ida da tsare-tsaren da aka ba su na yadda za su yi amfani da kason farko. Domin ana zargin cewa gwamnonin sun yi abinda suka ga dama da kudaden ko da yake gwamnati ba ta bayyana sunayen jihohin da suka yi gaban kansu da kudin ba.
To sai dai kuma yayin da ake fatan za'a bi ka'ida a wannan karon, tuni kungiyoyin ma’aikata da masu fashin baki suka soma tsokaci. Comrade Muhammad Baba Shelleng, dake zama jami’in hulda da jama’a na kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya, NULGE, reshen jihar Adamawa, yace su kam sun zura ido suga ko wannan karon za’a tuna dasu ganin cewa a baya an mance dasu.
Kamar yadda bayanai suka nunar, duk da dauki na bail-out,baya ga kason farko na kungiyar Paris Club, ta bada, har yanzu ma’aikata a wasu jihohin kasar na cikin mawuyacin hali na rashin samun albashi, batun da Mallam Yakubu Musa Uba, dake zama daya daga cikin shugabanin kungiyar wakilan kafofin yada labarai a Najeriya ke ganin akwai abun dubawa.
Domin Karin bayani, ga cikakken rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.
Your browser doesn’t support HTML5