Kungiyoyin Kwadago Kan Neman Gwamnatin Najeriya Ta Kara Mafi Karancin Albashi

BUHARI da MATAIMAKINSA

Neman karin mafi karancin albashi da kungiyoyin kwadagon Najeriya sukayi a ranar ma’aikata ta bana da alamu bai samu kwakkwarar amsa daga gwamnatin da ke famar karbar kasafin kudi, daga Majalisa da nufin fara wasu ayyuka da masu zabe zasu fara shaidawa.

Kamar yadda mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yace, muna cikin kalubale amma muradun gwamnatin mu shine inganta rayuwar al’umma. Wannana kalubalen na nunin karancin kudin shiga sakamakon faduwar darajar gangar fetur a kasuwannin duniya.

Wani lamari ma shine yadda bakin kungiyoyin kwadagon ya saba, uwar kungiyar LLC dake da hedikwata a Abuja na neman Naira dubu 56. Yan aware karkashin kwamarad Ajero na kungiyar ma’aikatar lantarki da ke da ofis a Lagos na neman Naira dubu 90.

Jami’in uwar kungiyar kwadago Nuhu Toro yace suna neman karin kudin ne duk bayan wasu shekaru kuma bisa doka. Inda yace a tsarin doka shine duk bayan shekara biyar kungiyar kwadago da gwamnati zasu zauna a sami masalaha, yanzu haka wa’adin shekaru biyar ya wuce don haka suke son a kara musu albashi mafi karanci na Naira dubu 56.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Kwadago Kan Neman Gwamnatin Najeriya Ta Kara Mafi Karancin Albashi - 2'57"