A yayin da jam’iyyun hamayya a jamhuriyar Nijer ke ci gaba da kalubalantar hukumar zaben kasar, shugabannin hukumar sun bayyana shirin damkawa kungiyoyin kasa da kasa kammalallan kundin rijistar, don ganin sun gudanar da aikin tace dukkan kura-kuran da ke kunshe a kundin kafin a soma buga katunan zabe.
Shakkun da wasu jam’iyyun siyasa ke nunawa game da tsare-tsaren zaben da hukumar CENI ta sa a gaba a yayin da ya rage saura watanni 5 a fafata a zaben gama garin kasar ya sa shugabanninta yanke shawarar damkawa kwararrun kungiyoyin kasa da kasa aikin tace kundin rajistar zaben kasar, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar Dr. Aladoua Alada ya bayyana a taron manema labaran da suka kira a karshen mako.
A tsakiyar makon jiya ne shugaban Nijer Issouhou Mahamadou ya gana da wani jami’in kungiyar kasashe masu amfani da harshen faransanci da ake kira OIF a takaice akan maganar tace kundin rajistar zabe, abinda ‘yan adawa suka ce ya sabawa ka’ida.
Shugaban hadakar jam’iyyun hamayya na FRDDR, Amadou Djibo Max a wannan sanarwa ya ce, muna hasashen cewa kura-kurai sun yi katutu a wannan kundin rajista. Ba mu san abinda ya sa shugaban kasa ke gaba-gaba akan wannan magana ta gudanar da aikin tace kundin zabe ba.
Ya kara da cewa, Shugaban kasar ba shi ne shugaban hukumar zabe ba, ba kuma shugaban CNDP ba, hakazalika ba shugaban wata jam’iyya ba. Ba mu san menene dalilinsa na nuna wannan bukata ba. Batun binciken kundin rajistar wani abu ne da daukacin jam’iyyun siyasa suka nuna bukata a kansa, a saboda haka Shugaba Issouhou ba shi da hurumin zaben kungiyar da za ta yi wannan aiki.
Tun a washegarin kafa hukumar zabe jam’iyyun hamayya ke zargin shugabanninta da zama ‘yan amshin shatan jam’iyyar PNDS mai mulki, lamarin da ya sa suke tunanin ba za su yi adalci a zaben da ake shirin gudunarwa a karshen shekarar 2020 ba.
Hukumar zaben ta sanar cewa a ranar 3 ga watan Satumba na shekarar 2020 za ta gabatar wa ministocin kula da sha’anin zabe kammalallen kundin rajista, kafin daga bisani ya shiga hannun jami’an bincike don soma ayyukan tacewa.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5