Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fadada Aikin Gwajin COVID-19 a Senegal


Gwajin COVID-19
Gwajin COVID-19

Kasar Senegal na fadada aikin gwajin cutar coronavirus don ba matafiya damar a gwada su kafin su bar kasar, da kuma wadanda ke isa kasar wadda ke yammacin nahiyar Afrika, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.

Kasar Senegal, da tattalin arzikinta ya dogara ga yawon bude ido don samar da kudin shiga kusan kashi 4 cikin 100 daga kayayyaki da ayyukan da ake yi a kasar duk shekara, ta ce mutum 9,422 suka kamu da cutar COVID-19 tun bayan barkewar annobar, mutum 182 kuma suka mutu.

Kusan mutane miliyan 1.7 suka je hutu a Senegal a shekarar 2019.

Kasar ta dage dokar hana tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa daga ranar 15 ga watan Yuli amma ta ce za ta hana ‘yan kasashen da suka hana ‘yan Senegal zuwa kasashensu shiga kasarta.

Ma’aikatar lafiyar kasar ta kaddamar da cibiyoyin gwajin cutar COVID-19 guda 4 a Dakar babban birnin kasar don gwada matafiya, wanda a lokacin da cutar ta barke guda daya ne kawai. Kasar na kuma shirin fadada gwaje-gwajenta a sauran wasu manyan garuruwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG