Gyaran da majalisar take son ta yi yana neman a cire kotun ne daga karkashin ikon sakataren gwamnati zuwa karkashin ma'aikatar shari'a.
Haka kuma gyaran na bukatar kotun ta zama wadda zata kaucewa siyasa.
Wannan matakin gyara dokar da ta kafa kotun ya dauki hankalin kungiyoyin kare hakkin jama'a ishirin da takwas har ma sun kira taron manema labarai a Abuja domin bayyana adawarsu da yukurin.
Eze Nwago shugaban kungiyar dake kare ka'idojin zabe yace menen ake gyarawa kuma don me ya sa za'a gyara yanzu. Me ya sa basu gyara da ba. Yace gyaran basa bukatansa yanzu musamman lokacin da shugaban majalisar ke gaban kotun yana fuskantar tuhuma.
Shi ma Kola Banwo shugaan wata kungiya ya yi tsokaci. Yace sabili da mutum daya da yanzu dokar ta shafa sai a yi yunkurin yiwa dokar kwaskwarima.Idan ana yawan canza dokoki ba gaira ba dalili to mulkin dimokradiya ya kare ke nan. Sai a gyara doka saboda mutum daya a kasar da take da mutane miliyan dari da saba'in bai dace ba.
Masu sharhi a alamuran yau da kullum su ma sun tofa albarkacin bakinsu. Mustapha Marafan Gayya yace bai kamata su bari irn wadannan rigingimun na faruwa ba. Misali ana cewa Bukola Saraki shugaban majalisar da Bola Tinubu uban jam'iyyar APC basa shiri. Ya kira 'yan APC su natsu su yi hadin kai.
Shi kuwa Bashir Baba ya yi mamakin yadda majalisar ta yi saurin kawo gyaran. Yace ko kunya bata ji ba. Bata tashi yin gyaran ba sai lokacin da Bukola Saraki shugabanta ya tsinci kansa a wani halin tafka rashin gaskiya kana ta san zata yi gyara. Wannan ya nuna 'yan majalisar dattawan ba jama'a suka zo su yiwa aiki ba suna yiwa kansu ne.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5