Kungiyoyin CAN Da IMN Sun Yi Na'am Da Matakin Amurka Kan 'Yancin Addini a Najeriya

Kungiyoyin addinai biyu a Najeriya sun yi maraba da matakin da Amurka ta dauka na sanya Najeriya a rukunin kasashen da ake zargi da saba ‘yancin addini.

Shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN da kungiyar ‘yan Shi’a da ake kira IMN a takaice sun ce mahukuntan Najeriya sun yi musu rashin adalci ta hanyar takura su. Mahukuntan kasar sun yi watsi da zargin sun kuma bayyana matakin na Amurka a matsayin wani sabani.

A wannan makon, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanya Najeriya da wasu kasashe 9 a matsayin kasashen da ake nuna damuwa akan abinda ya kira inda ake "saba ‘yancin addini sosai."

Wannan matakin na zaman na sharar fagen kakaba wa Najeriya takunkumi daga Amurka sai dai idan kasar ta inganta tsarinta na ‘yancin addini.

Ministan yada labaran Najeriya da kuma ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar sun fitar da sanarwa su na yin watsi da matakin na Amurka sun kuma ce za su tattauna da hukumomin Amurka don ganin an sauya matakin.

Amma kungiyoyin addini kamar ta Kiristocin Najeriya da ake kira CAN, sun ce matakin na nufin duniya na sane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya.

“A bayyane ya ke ba mu da ‘yancin addini. Kiristoci ba su da ‘yancin addinin da ya kamata su samu a Najeriya, idan aka yi la’akari da abinda ke faruwa, a cewar Cletus Usman, tsohon sakataren kungiyar CAN.

Wata kungiya da ita ma ta yi na’am da matakin na Amurka ita ce ta ‘yan Shi’a wato IMN.

Shekaru da yawa kenan kungiyar na yin kiran a sako mata shugabanta, wanda hukumomin Najeriya suka tsare bisa zargin rashin biyayya. Kungiyar ta kuma dora alhakin wani farmaki da ya yi sanadiyar kisan ‘ya’yanta fiye da 350 a shekarar 2015 a kan hukumomin Najeriya.