Kungiyoyin Arewa Sun Gujewa Shiga Zanga-zangar Juyin Juya Hali a Najeriya

  • VOA Hausa

Jami'an 'yan sanda sun tsaya kuwa da sakateriyar gwamnatin tarayya a Abuja.

A yayin da wasu ke shirin shiga zanga-zangar juyin juya hali a Najeriya, hadakar kungiyoyin matasan Arewacin Nigeriya mai suna Coalition of Northern Groups ta ce kada wani dan Arewa ya shiga zanga-zangar don akwai lauje cikin nadi.

Shugaban kungiyar Alhaji Nastura Ashir Sharif, wanda ke amsa tambayoyi a wajen taron manema labaru a garin Kaduna ya ce zanga-zangar ba ita ce mafita game da halin da Najeriya ke ciki ba.

A cewar Alhaji Nastura, “yanzu mun kai matsayin da wayewarmu da gogewarmu da yadda duniya ke tafiya yanzu, ko wacce irin matsala ce ta samu al’umma za a iya zaunawa a tattaunata a nemi masalaharta.”

Sai dai kuma shugaban hadakar kungiyoyin arewachin Najeriyan Ashir Sharif ya ce wajibi ne shugaban kasa Buhari ya yi gyara a tsarin tafi da gwamnatin sa.

Shirin shiga zanga-zangar na yau Litinin dai ya jawo cece-kuce tsakanin al’umma daga bangarori daban-daban, saboda ganin gwamnatin ta shugaba Buhari ba ta ma gama zama don cin wa'adin ta na biyu ba.

Domin Karin bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Arewa Sun Gujewa Shiga Zanga-zangar Juyin Juya Hali a Najeriya - 3'54"