Kungiyar yaki da cin hanci ta kasa da kasa Transparency International, ta kiyasta kimanin mutanen nahiyar Afirka miliyan 75 suka kasance cikin cin hanci da rashawa a shekarar da ta gabata, a wani rahoto da yake cewa yawancin ‘yan Afirka sunyi imanin cin hanci da rashawa na ‘kara kazancewa.
Masu bincike sun tambayi mutane sama dubu 43 dake nahiyar Afirka, kan saninsu da kuma yadda suke ganin cin hanci da rashawa. kashi 53 cikin dari na mutanen sunce sunyi Imanin cewa cin hanci da rashawa ya karu a kasashen su cikin watanni 12.
Yawacin shugabannin Afirka sunyi kamfen ne da ‘daukar alkawarin shawo kan matsalar cin hanci da rashawa, amma da alamu har yanzu matsalar na kara yawaita a nahiyar Afirka.
Da yawa mutanen da akayi wannan bincike da su, sun fito ne daga kashen Afirka 18 kuma sunce gwamnatocin su basa tabuka abin kirki wajen yaki da cin hanci da rashawa, musammam ma yafi yawa ga jami’an kotu dana ‘yan sanda.