Kungiyar Yaki Da Bauta a Nijar, Timidria, Za Ta Kai Kara A CEDAO

Wata tsohuwar baiwa a Indiya

A cigaba da kokarinta na yaki da bauta a Janhuriyar Nijar da makwabtan kasashe, kuniyar yaki da bautar da mutane, Timidria, ta lashi takobin kai wani batu na bautar da wata mace ga kotun CEDEAO.


Kungiyar yaki da bauta a jamhuriyar Nijar ta bayyana shirin shigar da kara a gaban kotun CEDEAO da nufin kwato hakkin wata mata ‘yar asalin kasar Nijar, wacce ta shafe shekaru sama da 30 a wani kauyen Burkina Faso a matsayin baiwa .

Wakilin muryar Muryar a Yamai Sule Mummuni Barma, wanda ya aiko mana da rahoton, ya ce 'yan kungiyar ta Trimidria sun yi nuni da cewa a karkashin wata al’adar karkarar Bankilare da ke yankin Tilabery ne wani basaraken gargajiya ya baiwa ‘yarsa kyautar Malama Fodi Mohammed domin yi ma ta aikace aikace a kauyen Gorom-Gorom na Burkina Faso, inda daga bisani aka mayar da ita tamkar wata uwar garke ta wajen sa ta cudanya da mazaje iri iri wadanda ta haifi ‘yaya 8 da su kamar yadda Sakataren kungiyar Timidria Ali Bouzou ya bayyana wa manema labarai.

‘Yar kimanin shekaru kusan 40 Malama FodiI yanzu haka na shayar da wata jaririyar da ba ta fi wata 3 da haifuwa ba sai wata mai shekaru biyu da ta ke jaye da ita yayinda rashin ganin sauran ‘yayanta ke daga mata hankali inji ta, lamarin da ya sa ta bukaci hukumomi su yi wani abu a kai.

Ainahi iyayen Malama Fodi na daukar kansu a matsayin bayi mallakar sarakunan abzinawan Bankilare, lamarin da a yau ke shafar ‘yaya da jikokinsu kamar yadda a yanzu ya rutsa da wannan baiwar ALLAH inji wani kawunta, Malam Amidigi Saibou.…

Kungiyar TIMIDRIA wace ta yi Allah wadai da faruwar wannan al’amari a kasashen da aka haramta bautar da dan adam, ta kudiri aniyar shigar da kara a gaban kotun ECOWAS da na sauran kotunan kasa da kasa don ganin an hukunta masu hannu a abinda ta kira aika aika.

A shekarun baya kotun CEDEAO da ke Abujan Najeriya ta caji gwamnatin Nijer miliyoyin cfa a matsayin tara bayan da kungiyar TIMIDRIA ta shigarda kara akan halin bautar da wata mata mai suna Kadijatu Mani Korau ta tsinci kanta ciki.

Ga wakilinmu Sule Barma da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Yaki Da Bauta Za Ta Kai Kara CEDEAO